Alamomin Cutar Murar Mashaƙo Cutar murar mashaƙo ta na saurin kisa

  Diphtheria cuta ce wacce ake saurin ɗaukarta wadda ƙwayar cutar bacteria mai suna "corynebacterium diphtheriae" take haddasa wa....

 Maganin murar mashaƙo


Diphtheria cuta ce wacce ake saurin ɗaukarta wadda ƙwayar cutar bacteria mai suna "corynebacterium diphtheriae" take haddasa wa. Tana kama hanyoyin numfashi ne waɗanda suke daga maƙogwaro zuwa ƙirji, sai ta haifar da matsalar sarƙewar numfashi. Haka kuma, takan iya kama sassan fatar jiki ta haddasa ƙuraje masu gunɗar ruwa.

Alamomin Cutar Murar Mashaƙo 

Cutar murar mashaƙo ta na saurin kisa saboda ba a saurin gane ta da wuri idan an kamu, kuma a mafiyawanci sai ta kai ga yaro ya fara numfashi cikin wahala, ko kuma ya gaza cin abinci ko ya kamu da zazzabi mai tsanani ko kuma yawan tari sannan ake fara tuhumar cutar. Ga wasu alamomi na cutar murar mashaƙo;

Murar Mashaƙo

  1. Kumburin wuya
  2. Sarkewar numfashi
  3. Zazzabi
  4. Rashin ƙarfin jiki
  5. Rashin iya haɗiye yawu ko chin abinci
  6. Ƙurajen jiki
  7. Yawan tari
  8. Yoyon hanci
  9. Jajayen ido da dai sauransu. 

Yadda Ake Kamuwa Da Cutar Murar Mashaƙo 

Ana daukar cutar murar mashaƙo ta hanyar shaƙar iskar tari, numfashi ko atishawar da mai cutar yayi. Sannan ana iya kamuwa da ita ta hanyar mu'amalar cuɗanya da mai cutar, ko kuma yin amfani da kwano, cokali, kofi, da sauran kayayyakin gida waɗanda mai cutar yayi amfani dasu.

Hanyoyin Kariya Daga Cutar Murar Mashaƙo 

1. Yin allurar rigakafinta cutar, watau "diphtheria, tetanus, pertussis - DTaP" waɗanda ake yiwa yara a lokacin da suke jarirai, kuma ake ƙara yin su saboda ƙarfafa garkuwar jiki (booster dose) idan mutum ya girma.

2. Kyautata tsaftar jiki, abinci, tufafi, da muhalli.

3. Wanke hannaye da ruwa ko sabulu idan mutum yayi atishawa ko yayi mu'amala da mai cutar.

4. Kaucewa zama wuri ɗaya da mai cutar.

5. Rufe hanci da baki a lokacin da mutum zaiyi tari ko atishawa. 

6. Sanya takunkumi (face mask) a lokacin da mutum zai shiga muhallin da annobar cutar ta ɓarke.

7. Killace waɗanda cutar ta kama a wurin jinya sa kuma hana su cuɗanya da sauran jama'a.

Rigakafin Gaggawa Ga Wanda Ya Kamu Da Cutar Murar Mashaƙo 

1. Ya wajaba a kebe shi daga cudanya da mutane masu lafiya.

2. A gaggauta zuwa asibiti dashi domin samun kulawar likita ta gaggawa.

3. A sanya masa takunkumi saboda rage yawan fallatsar ruwan tari da atishawar sa a cikin muhalli.

Yadda Ake Maganin Cutar Murar Mashaƙo A Asibiti

1. Yin amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cuta na antibiotics kamar su penicillin, erythromycin, da sauransu.

2. Yin amfani da magungunan kashe guba na"diphtheria antitoxin" domin dallashe kaifin dafin cutar a jiki. 

3. Yin amfani da magungunan da zasu taimaka wajen farfaɗowar maras lafiyan kamar iskar oxygen, kwayoyin kashe raɗaɗi, karin ruwa na drips da dai sauransu.

COMMENTS

Name

Blaa,1,Te,1,Test,2,Yeaa,1,
ltr
item
LAFIYATA.COM.NG: Alamomin Cutar Murar Mashaƙo Cutar murar mashaƙo ta na saurin kisa
Alamomin Cutar Murar Mashaƙo Cutar murar mashaƙo ta na saurin kisa
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgNSeKlNAr5K5E5dys3P0xnspsxwhH_uof3ctz22N9m460NvcaKFQLkQKzouQ-rIFw37oxe64kq88NI2aI96McWQIVc5uopRdxgy_q1bFSl9P-iKkLd6AmIMIHs_ov6N5y7GgxhpFL9jn9UbFSeeZCZQP2yLovYrHhWeAQ4VGSlMbXiJybQdBTMuriCCgs/w320-h198/image-429.png
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgNSeKlNAr5K5E5dys3P0xnspsxwhH_uof3ctz22N9m460NvcaKFQLkQKzouQ-rIFw37oxe64kq88NI2aI96McWQIVc5uopRdxgy_q1bFSl9P-iKkLd6AmIMIHs_ov6N5y7GgxhpFL9jn9UbFSeeZCZQP2yLovYrHhWeAQ4VGSlMbXiJybQdBTMuriCCgs/s72-w320-c-h198/image-429.png
LAFIYATA.COM.NG
https://draliero.blogspot.com/2024/09/alamomin-cutar-murar-mashao-cutar-murar.html
https://draliero.blogspot.com/
https://draliero.blogspot.com/
https://draliero.blogspot.com/2024/09/alamomin-cutar-murar-mashao-cutar-murar.html
true
5016444998716573213
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy Table of Content